أشترك معنا وأقرأ الرسائل الجامعية وأصدارات الدار

SUNAYEN HAUSAWAN NIJERIYA DA NAMISIRAWAN MASAR NA GARGAJIYA A CIKIN TSARIN ABAJADIN HAUSA

Be the first to review this product

التوفر: In stock

$6.00

Quick Overview

Bismillahir Rahamanir Rahim.
Da sunan Allah mai rahama da jinqai, na fara buxe bayanin taririn rayuwa ta. Tsira da amincin Allah su tabbata a kan Annabinmu Muhammadu(SAW) tare da Alayensa da Sahabbansa da Tabi'ansa da Tabi'ittabi'ansa da kuma xaukacin dukkan Musulmai, rayayyu da waxanda suka riga mu gidan gaskiya. Da fatan Allah ya qara xaukaka addinin Musulunci da Musulmai baki xaya. Allah ya qara shiryar da shuwagabanninmu, ya qara sanya su tausaya mana. Allah ya qara rufa mana asiri duniya da lahira, amin.
An haifi Malam Abdulrahaman Ado a unguwar Tsohuwar Kasuwa ta Malumfashi a shekarar 1963. Ya yi Firamare a S.P.S., Sallau (1971-76). Ya yi Sakandare a G.S.S.Maqarfi (1976-81). Ya yi Kwalejin Nazari mai Zurfi (C.A.S.), a Zariya(1982-84). Ya yi Digiri na xaya a Hausa, a Jami’ar Bayero, Kano(1984-87). Ya yi nazarin Difiloma ta "Gaba da Digiri ta Ilimin Koyarwa" (PGDE) (1997-98) a UDUS, Sokoto. Ya yi nazarin "Qaramin Matakin Sanin Harshen Larabci" (J.C.I.A.)(2003-04) a UDUS, Sokoto. Ya yi ilimin Difiloma ta "Na’ura mai Qwaqwalwa" (2008), a UDUCONS, Sokoto. Ya yi Digiri na biyu a Hausa (2006-2009), a Jami’ar Usumanu Xanfodiyo, Sakkwato.
Mallam Abdulrahaman ya fara yin aikin koyar da Hausa Makarantar Firamare ta Unguwar Dutse, Malumfashi (1981). Ya yi aikin hutun Xalibai a Babban Kotun Shari’a ta Malumfashi (1983). Ya koyar da Hausa a aikin Koyarwar Wocin-Gadi, a G.S.S. Malumfashi (1984). Ya kasance cikin aikin koyar da Hausa a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ke a Azare (1988-1995) da Kazaure (1995-1996) da Sakkwato (1996-2008) da kuma Daura 1988-2009). Ya yi aikin koyar da Hausa, "Koyarwar Bayan Fage", a Sakandaren Gwaji ta Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato (2002-03) da kuma Sakandaren Kuxi (mai zaman kanta), Mai Alamar Jaririn Wata, Mai Launin Shuxi (Blue Cresent), Sakkwato (2003-04). Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina ta xauke shi aikin koyar da Hausa a shekara 2009, a bisa jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi. Jami’ar Umaru Musa, Katsina ta tura shi zuwa karatun Digiri na uku, a Jami’ar Alqahira, a shekarar 2011.
Mallam Abdulrahaman ya riqe muqamai da yawa waxanda ake bayarwa a cikin makarantun Kwalejojin Tarayya da kuma na cikin Jami’a. Ya halarci kwasa-kwasai da yawa na sanin makamar aikin koyarwa da Hukumar Ilimi Ta Gwamnatin Tarayya ke shiryawa a makarantunta na duk faxin Nijeriya. Ya shugabanci yin gyaran jarrabawar kammala Sakandare, ta hukmar WAEC da NECO a Sakkwato(2000-2009).Ya yi wa hukumar Jarrabawa ta qasa, wato Neco, aikin "Rubuta Samfurin Jarrabawar Qarshe ta Sakandare", tambayoyi da amsoshi (2007).Ya zama mamba na WAEC, na "Gyaran Manhajar Karatu a Sakandarori" (2008). Shi mamba ne na "Hukumomin Karantarwa da Koyarwa", watau NINLANG, Aba da TRC da ASCSN da ASU.
Mallam Abdulrahaman mutum ne mai son yin karance-karance da rubuce-rubuce, wanda a sanadiyyar haka ya gabatar da qasidu guda goma, a tarurrukan qara wa juna sani, a kwalejoji da jami’o’i. Wasu an wallafa su a cikin littattafai da mujallu na kwalejin Gwamnatin Taryya ta Sakkwato da Kwajejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya ta Katsina da Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zuba, Abuja. Wasu qasidun nasa kuma, ya karvi takardun shedar za a buga su a cikin mujallu da littafai na Jami’o’in Bayero, Kano da Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato da Ummaru Musa Yar’adua, Katsina da Jami’ar Alqahira.
Haka kuma, Mallam Abdulrahaman ya fita qasashen waje sau uku. Na farko, ya je Haji a shekarar 2006, sannan ya je ziyazar aiki, tare da xaliban Sashen Harsunan Nijeriya na Umaru Musa Yar’adua, Katsina, zuwa Jami’ar Abdulmuminu, Nijar, daga nan kuma sai tafiya zuwa karatun digiri na uku a Jami’ar Alqahira.
Malam Abdulrahaman ya karvi kyaututtuka na qwarewa a wajen koyar da Hausa a Barno(1988) da Sakkwato 1997 da 1998). Ya sami takardar yabo ta yin aikin shugabanci ingantacce a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwato(2008).
A yanzu, Malam Abdulrahaman yana da mata xaya da ‘ya’ya biyar. Yana yin hutun “Jaki da kaya a ka”, watau hutun karatun yin Digiri na uku a Jami’ar Alqahira.
Hausawa na cewa: “Bawan Allah, da sannu rayuwarsa ke tafiya cikin nasara”. Alqawarin Allah ne cewar: “Bayan wuya, to, lallai daxi na nan zuwa”. Muna nan muna sa rai! Ko a duniya ko a lahira. Ba mu gajiya da jiran tsammani na Allah. Masu hikima na cewa: "Malamin Makaranta ! Sakamakonka na Aljanna!" Allah ya rabauta mu da Aljanna Firdausi, amin.
Muna godiya ga Allah bisa rahamonin da ya yi mana, waxanda muka sani da waxanda ba mu sani ba. Alhamdulillah!

Malam Abdulrahaman Ado
Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami'ar Umaru Musa Yar'adua,
Katsina,
Nijeriya.

SUNAYEN HAUSAWAN NIJERIYA DA NAMISIRAWAN MASAR NA GARGAJIYA A CIKIN TSARIN ABAJADIN HAUSA

Double click on above image to view full picture

Zoom Out
Zoom In

More Views

  • SUNAYEN HAUSAWAN NIJERIYA DA NAMISIRAWAN MASAR NA GARGAJIYA A CIKIN TSARIN ABAJADIN HAUSA

* Required Fields

$6.00

Details

ABUBUWAN DA KE CIKI Bangon Littafi Taken Littafi Faxakarwar Haqqin Mallaka Abubuwan Da Ke Ciki Taqaitaccen Tarihin Rayuwar Marubucin Littafin Sadaukarawa BABI NA FARKO BAYANIN MASANA A GAME DA LITTAFIN Tofa Albarkacin Baki Daga Farfesa Ashraf El-Azzazi Bayanin Shugaban Sashen Harsunan Afirka Farfesa Muhammad Noufal Muqaddimar Dr Samir Ezzat Jawabin Edita Taqaitaccen jawabin Mataimakiya Malama Lamiaa Sa'ad El-Khouly Godiya BABI NA BIYU BAYANIN YADDA AKA GUDANAR DA BINCIKEN LITTAFIN Tarihin Bincike A Kan Littafin Hanyoyin Gudanar Da Bincike Sunayen Hausawa Na Gargajiya Sunayen Larabawan Misira Na Garagajiya Manufar Wannan Bincike Dalilin Yin Bincike Matsalolin Bincike Matsalar Samun Takardar Daidaiton Karatu A Misira Matsalar Fassara Matsalar Kashe Kuxi Matsalar Bincike Cikin Baquwar Al'umma Matsalar Karin Harshe BABI NA UKU SUNAYEN HAUSAWA NA GARGAJIYA Ma'anar Suna Tarihin Sunayen Hausawa Na Gargajiya Sunayen Hausawa Na Gargajiya A Cikin a Abajadin Hausa Sunayen Hausawa Na Gargajiya masu Farawa da Harafin «A» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «B» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «C» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «D» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «X» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «F» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «G» Sumayen Hausawa Na Gargajiya Masu Farawa Da Harafin «H» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «I» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «J» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «K» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «L» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «M» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «N» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «R» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «S» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «T» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «U» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «W» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «Y» Sunayen Hausawa Na Gargajiya Masu farawa Da Harafin «Z» BABI NA HUXU SUNAYEN LARABAWAN MISIRA NA GARGAJIYA Taqaitaccen Bayani A Kan Sunayen Misirawa Na Gargajiya Yadda Misirawa Ke Yin Raxin Suna Na 'Ya'yansu Sunayen Misirawa Na Gargajiya A Cikin Abajadi Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «A» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «B» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «D» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «E» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «F» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «G» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «H» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «I» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «J» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «K» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «L» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «M» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «N» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «O» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «R» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «S» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «T» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «U» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «W» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «Y» Sunayen Misirawa Na Gargajiya Masu Fara Da Harafin Harafin «Z» BABI NA BIYAR Naxewa Da Shawarwari Naxewa Shawarwari Manazarta

Product Tags

Use spaces to separate tags. Use single quotes (') for phrases.